bayyinaat

Published time: 09 ,April ,2018      01:03:42
Musulmi sun hadu gaba dayansu a kan cewa Allah Ta’ala ya shar’anta wannan aure a cikin addinin musulunci, babu mai jayayya a cikin hakan daga malaman mazhabobin musulunci duk da sabaninsu, sai dai asalin shar’antawar ta shi ta hadu da larurori, sannan Alkur’ani mai girma yana nuni akan shar’antawarsa, kamar yadda ruwayoyi masu inganci sun tabbatar da shar’antawarsa, har ma wadanda suke da’awar canja hukuncinsa.
Lambar Labari: 109
Fassarar Littafin Mutu'a na Majma'ul Aalami li Ahlil bayt
Auratayya a shari’ar musulunci ta tsayu a mahanga biyu.
Na farko: Auren Da’imi wanda ake la’akari da shi a mafi girman abin da musulunci ya assasa, wannan shi ne mahangar shari’a ta farko ta fannin auratayya.
Na biyu: Auran mutu’ah shi ne majinginar aminci da yake katange al’umma daga fadawa cikin sharrin zina, a lokacin da ba a samu abin yin auren  din –din –din ba,ko kuma an samu abin yin sai dai dalilai na hankali ko na shari’a suka janyo yin hakan.

Shi auran mutu’ah yana tarayya da ainihin auran din - din –din ta fuskar sarrafa sha’awa ta hanyar halal, da kariya ga nasabobi da katange rashin cakudewar nasabobin, da kuma kulawa da gundarin kamewa da kunyata a cikin al’umma, da ba da dama ta fuskar wasu al’umura na daban wanda ba za a ce musu aure ba. A cikin auratayya irin na mutu’ah, kulla aure, sadaki da iddah da lokacin karewa kayyadadde ne, kuma babu gado da ciyarwa a cikin sa.
Irin wannan nau’in na aure tabbatacce ne a bangaren shari’a da nassi daga littafi mabuwayi da sunnah madaukakiya,  babu wani a cikin musulmi da ya saba da tabbatuwarsa a shari’a lokacin manzo (s.a.w.a).Duk abin da ya faru a cikin wannan al’amari na sabani daga khalifa na biyu ne Umar dan khaddabi, ya yi hani a kan sa kuma ya azabtar, yan makarantar khalifofi sun bi shi suna masu dogaro da mafararshi, suna masu cewa  suna bin sunnar khalifofi  ne, akwai daga cikin su wanda da suke cewa an shafe hukuncin farko a kan shi,(auren mutu’a). Saboda dalilin canza matsayin mutu’a sai aka samu bayyanar da’awowi masu yawa, daga cikinsu akwai: cewar wai hanin ya faro ne lokacin Manzo Allah (s.a.w.a) da kan shi wai al’kur’ani ya canja ayar mutu’a.
Saboda haka bayyanar da hakika a wannan al’amari na mutu’a a shari’a muhimmi ne babba wanda ba makawa sai mun kawo wadannan abubuwa guda uku:
Maganar farko: Auratayyar mutu’a a cikin Alkur’ani da Sunnah.
Magana ta biyu: Shin an canja hukuncin auren mutu’ah?
Magana ta uku: Matsayin sahabbai da tabi ‘ai dangane da auran mutu’ah.

MAGANAR FARKO:
Auran mutu’a a alkur’ani da Sunnah.
Musulmi sun hadu gaba dayansu a kan cewa Allah Ta’ala ya shar’anta wannan aure a cikin addinin musulunci, babu mai jayayya a cikin hakan daga malaman mazhabobin musulunci duk da sabaninsu, sai dai asalin shar’antawar ta shi ta hadu da larurori, sannan Alkur’ani mai girma yana nuni akan shar’antawarsa, kamar yadda ruwayoyi masu inganci sun tabbatar da shar’antawarsa, har ma wadanda suke da’awar canja hukuncinsa.
Dangane da littafin Allah mabuwayi: Allah (s.w.t) Yana cewa "wadanda kuka ji dadi da su (mata) ku ba su ladaddakinsu mai yawa”(1).
Ubaiyu dan Ka’ab, da  dan Abbas, da Sa’idu dan Jubair da dan Mas’ud da Sadiy sun kasance suna karantawa "wadan da kuka ji dadi da su (mata) zuwa wani lokaci abin Ambato” Dabari ya fitar da wannan daga gare su a cikin tafsirin ayar a cikin tafsirul kabir (nashi), Zarkashi ya dauki wannan ruwayar a matsayin mursal, (mursali musallam) haka nan Arrazi a cikin tafsirinsa, da sharshin sahihul Musulim na annawawiy a cikin farkon babin Auren mutu’a.
1.  Suratul Nisa’i-23
Imam Ahmad bin hanbali ya karfafa shi a musnad din shi, da Abubakar Jasasi a cikin littafin Ahkamul-kur’an, da Abubakar Baihaki cikin sunanul-kubra, da Alkali Bairawiy cikin tafsirinsa,da Ibn kasir a cikin tafsirinsa,da Jalaludden suyudi a cikin durur-mansur.
Da Alkali Asshaukaniy a cikin tafsirinsa da Shihabuldeen Alusiy cikin tafsirinsa cewa dalilin saukar wannan ayah a bigiren mutu’a ne, da madogarar da take karewa ga Ibn Abbas, Ubayyu dan ka’ab, da Abdullahi dan Mas’ud da Imran da Huseeyn, da Habibu dan Sabit daga sahabai.
Da sa’idu da Jubair da Katadata da Mujahid daga tabi’ai daga Ibn Abbas.
Ba zai yi wu ba a fassara ayar da auren da’im ba kamar yan da mai tafsirin almanar ya bayyanar, saboda dalilai masu zuwa:
Daga abin da ya gabata na adadin sahabban da suke karanta ayar "wadanda kuka ji dadi da su  ku ba su ladaddakinsu mai yawa” tare da Karin jimla mai bayani a tsakiya "izuwa lokaci kayyadadde”da manufarsu daga ayar na bayanin  da ma’anar tafsirin,wannan jimla mai bayani ba za ta yi dace ba sai dai tare da auren mutu’ah.

Lafazin mutu’a; duk da za a iya amfani  da shi a auren da’imi sai dai ma’anarsa ta bayyana ne  a kan auren mut’ah, kamar yadda lafazin aure duk da cewa zai inganta a yi amfani da shi a auren mutu’ah  sai dai ma’anarsa a auern din-din-din yafi bayyana.Saka lafazin mutu’ah a cikin ayar zai taimaka wajen tafsirinta da auren mutu’ah ba na da’imi ba,ko da a ciki bai bayyana ma’anar ba,ba za mu takaita ba wajen dalilin shi a kan auren mutu’ah.A nan sai ya kasance cikin lafuzzan ma’anoni da yawa wadanda ake iya amfani da su a cikin ma’ana fiye da daya.
Ita ayar ta zo ne a cikin surar Nisa’i wadda ta fara da ambaton auren din-din-din da hukuce-hukucensa a cikin aya ta3 da ta 4 da aya ta 20 zuwa ta 23,idan abin da ake nufi tumatu’i shi ne auren din-din-din har ila yau ayar za ta kasance an maimaita ta domin abin da ake neman ambatonsa a cikin abin da ya gabata na daga surar.
Da a ce mutu’a ta kasance da ma’anar auren din-din-din, to mene ne manufar cewa an shafe ta a nan? Shin ma’anar shafewar shi ne auren din-din-din? Saboda haka wannan ikirarin shafewar zai zama yana karfafa kasancewar ayar mutu’ah da ma’anar auren din-din-din.
Amma nassosin hadisai mutawatirai (wanda masu ruwayarsu suke da yawa)masu yawa ne sosai,za mu yi nuni izuwa ga sashensu.
1. Daga Jabir, ya ce mun kasance muna auren mutu’ah a zamanin Manzon Allah           (s.a.w.w) da zamanin Abubakar sannan Umar ya hana. (1)
2. Daga Ibn Abbas: lallai ayar mutu’ah tana hukunci ba ta zamo shafaffiya. (2)
3. Mun kasance muna auren mutu’ah zamanin manzon Allah (s.a.w.a) da           Abubakar da rabin kalifancin Umar sannan sai Umar ya hana. (3)
4. Daga Hakim da ibn Jarih da wasunsu, suna cewa: Imam Ali (as) yana cewa "Ba don Umar ya hana auren mutu’ah ba, ba wanda zai yi zina sai shakiyyi. (4)
5.Daga Imran da Hussayn yana cewa: ayar mutu’ah ta sauka ne a cikin littafin Allah Ta’ala.Ba wata aya da ta sauka don shafe ta, Manzon Allah(s.a.w.a) ya umarce mu da ita,mun yi mutu’a lokacin manzon Allah(s.a.w.a.)har ya bar duniya bai hana mu ba,sannan sai wani mutum ya fadi ra’ayinsa.(5)
6. A karshe an ruwaito daga ibn Jarih shi kadai hadisai goma sha takwas a kan halascin auren mutu’ah (6) balle sauran ruwayoyi.



1. Sahihul Muslim 4:131 daba’in maskul, musna Ahmad 6:405, Fahul Bariy 9:149
2. Alkashaf 1:498 dab’in Berut, Algadir Akan tafsirin kazina 1:307.
3. Bidayatul Mujtahida 2:58, El-gadir 7:223, 207.
4. Tafsiril Dabariy 5:9, tafsiril Raziy 10:50, Durur Mansur 2:140.
5. Sahihul Buhari 2:168, 6:3, Sahihul Muslim 4:48, S.Nisa’I 5:155, M.Ahmad 4:426.
6. Nailil anwar 6:271, fathul Bari 9:10.

Hadisai da nassosi suna karfafa abin da ayoyi masu girma sukai nuni na halascin auren mutu’ah, kuma hukuncinsa yana nan daram.Haramcinnsa kuwa ya samu ne daga Umar (ba daga Annabi ba (s.a.w.a).Sannan wasu daga sahabbai da tabi’ai kai har ibn Umar da kansa shi ma ya tafi a kan halascin auren mutu’ah tare da cewa Umar ya hana.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: